ABNA24 : Bayanai sun ce ba’a kai ga fitar da bayanai ba game da adadin mutanen da suka mutu, amma ana fargabatar cewa adadin wadanda suka mutu a hatsarin jirgin ruwan zai iya kaiwa 100.
Amma an yi nasara ceto mutane 22 da ransu, yayin da ake ci gaba da gudanar da ayyukan ceto.
Mai magana da yawun hukumar ’yan sandan jihar Kebbi, Nafiu Abubakar, ya shaidawa masu aiko da rahotanni cewa, hukumar ’yan sandan ta samu bayanin cewa jirgin ruwan dauke da fasinjoji sama da 160 ya kife a tekun River Niger yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kebbi mai makwabtaka da jahar Neja.
Wasu rahotanni na daban sun hadarin ya faru ne sakamakon darewar jirgin ruwan sakamakon yi masa lodin da ya wuce kima.
342/